Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Demons

28 ayoyi · 15 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’

  2. “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’

  3. “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”

  4. “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.

  5. Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.

  6. Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”

  7. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,

  8. “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”

  9. Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

  10. Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, “Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?

  11. In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.

  12. In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.

  13. In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.

  14. Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa.

  15. Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi.

  16. Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”

  17. Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

  18. Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”

  19. Ya amsa ya ce, “Sai da addu’akaɗai irin wannan yakan fita.”

  20. Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.”

  21. ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.

  22. Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”

  23. Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.

  24. A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu.

  25. Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu.