Tsallake zuwa abun ciki

Satan

55 ayoyi

An kuma san shi da: Beelzebub

Ayoyin da suka ambaci Satan

Tace bisa littafi
  1. Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba.

  2. Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka.

  3. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.

  4. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.

  5. Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,