Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru,

  2. Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa.

  3. Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa.

  4. Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”

  5. Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”

  6. Har wa yau, ina da tambaya. Shin, Isra’ila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce, “Zan sa ku yi kishin waɗanda ba al’umma ba; zan sa ku yi fushin al’ummar da ba ta da fahimta.”

  7. Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka?

  8. An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.

  9. To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce,

  10. Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa.

  11. Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu.

  12. Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.

  13. Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.

  14. An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.

  15. Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.

  16. Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba?

  17. Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba.

  18. Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”

  19. Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.

  20. Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.

  21. Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna.

  22. Ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake, har Musa ya ce, “Ina rawar jiki don tsoro.”

  23. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”

  24. suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai.