Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi.

  2. Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.

  3. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.

  4. Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”

  5. Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci.

  6. To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?

  7. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?”

  8. Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”

  9. Gama Musa ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai tasar muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku; dole ku saurari duk abin da ya faɗa muku.

  10. Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”

  11. Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”

  12. “A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa.

  13. Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.

  14. Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ’ya’ya biyu maza.

  15. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  16. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.

  17. “Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.

  18. “Wannan Musa ne ya ce Isra’ilawa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’

  19. Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba!’

  20. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.

  21. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.

  22. Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”

  23. Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”

  24. Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”

  25. An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.