Tsallake zuwa abun ciki

Miriam

12 ayoyi · 4 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Miriam

  1. Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.

  2. Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.”

  3. Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.

  4. Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.

  5. Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,

  6. Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;

  7. Haka aka fitar da Miriyam bayan sansani kwana bakwai, mutane kuwa ba su ci gaba da tafiya ba sai da aka dawo da ita.

  8. A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta.

  9. sunan matan Amram shi ne Yokebed, ita zuriyar Lawi ce, wadda aka haifa wa Lawiyawa a Masar. A wajen Amram kuwa ta haifi Haruna, Musa da kuma ’yar’uwarsu Miriyam.

  10. Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Miriyam a hanya, bayan kun fito Masar.

  11. Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.

  12. Na fito da ku daga ƙasar Masar na kuma ’yantar da ku daga ƙasar bauta. Na aika da Musa yă jagorance ku, haka ma Haruna da Miriyam.