Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarta. Ya ɗaga sandansa a gaban Fir’auna da bayinsa, ya bugi ruwan Nilu, dukan ruwan kuwa ya zama jini.

  2. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.

  3. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’ ”

  4. Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Yi addu’a ga Ubangiji yă ɗauke kwaɗi daga gare ni da mutanena, zan kuwa bar mutanenku su tafi su yi hadaya ga Ubangiji.”

  5. Musa ya ce wa Fir’auna, “Na ba ka dama ka ba da lokacin da zan yi addu’a dominka da kuma bayinka da mutanenka, gidajenku kuwa za su rabu da kwaɗi, amma ban da waɗanda suke cikin Nilu.”

  6. Bayan Musa da Haruna sun bar Fir’auna, Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji saboda kwaɗin da ya kawo a bisa Fir’auna.

  7. Sai Ubangiji ya yi abin da Musa ya nema. Kwaɗin suka mutu a gidaje, da filaye, da kuma gonaki.

  8. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.”

  9. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.

  10. Sai Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tafi, ku miƙa hadaya ga Allahnku, a nan a cikin ƙasar.”

  11. Amma Musa ya ce, “Wannan ba zai yiwu ba. Hadayun da mukan miƙa wa Ubangiji, Allahnmu haram ne ga Masarawa. In kuwa muka miƙa hadayun da suke haram a idanunsu, ba za su jajjefe mu ba?

  12. Musa ya amsa, “Da zarar na bar ka, zan yi addu’a ga Ubangiji, gobe kuwa ƙudaje za su bar Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa. Sai dai a tabbata Fir’auna bai sāke yin ruɗi ta wurin ƙin barin mutane su tafi su miƙa hadayu ga Ubangiji ba.”

  13. Sa’an nan Musa ya rabu da Fir’auna, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,

  14. Ubangiji kuwa ya yi abin da Musa ya roƙa. Ƙudaje suka rabu da Fir’auna da fadawansa da kuma mutanensa; ba ƙudan da ya rage.

  15. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, “Ka bar mutanena su tafi, domin su yi mini sujada.”

  16. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ɗibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa tokar sama a gaban Fir’auna.

  17. Sai suka ɗibi tokar matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna, Musa ya watsa ta a iska, sai marurai masu zafi suka fiffito bisa mutane da dabbobi.

  18. Bokaye suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran da suke bisansu da a kan dukan Masarawa.

  19. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa.

  20. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada,

  21. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.”

  22. Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;

  23. Sai Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “A wannan karo na yi zunubi. Ubangiji, shi ne da gaskiya, ni da mutane mu ke da kuskure.

  24. Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.

  25. Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.