Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Travellers

110 ayoyi · 39 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”

  2. Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi.

  3. A rana ta huɗu suka tashi da sassafe ya kuma yi shiri yă tafi, amma mahaifinta yarinyar ya ce wa surukinsa, “Ka ɗan ci wani abu don ka sami ƙarfi; sa’an nan ka tafi.”

  4. Sa’ad da ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, sai tsohon ya yi tambaya ya ce, “Ina za ku? Ina kuka fito?”

  5. Muna da ƙara da abinci don jakunanmu, muna kuma da burodi da ruwan inabi dominmu da bayinka, ni, baiwarka da kuma saurayin nan tare da mu. Ba ma bukatar kome.”

  6. Tsohon ya ce, “Na marabce ku a gidana. Bari ni ba ku duk abin da kuke bukata. Kada ku dai kwana a dandali.”

  7. Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.

  8. Maigidan ya fita waje ya ce musu, “A’a, abokaina, kada ku yi abin kunyan nan. Da yake mutumin nan baƙona ne, kada ku yi rashin kunyan nan.

  9. Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.

  10. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,

  11. su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!

  12. “Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.

  13. Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”

  14. Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.

  15. Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.

  16. Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”

  17. Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.

  18. Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.

  19. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.

  20. Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su.

  21. Barzillai mutumin Gileyad shi ma ya zo daga Rogelim don yă ƙetare Urdun tare da sarki, yă kuma sallame shi daga can.

  22. Ta iso Urushalima da tawaga mai yawa, tare da raƙuma masu ɗauke da kayan yaji, da zinariya masu yawa, da duwatsu masu daraja. Ta zo wurin Solomon ta kuwa yi magana da shi game da dukan abin da take da shi a ranta.

  23. Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.

  24. Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

  25. Sai ta sa wa jakar sirdi ta ce wa bawanta, “Yi ta kora mini jakar, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”