Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nabal

37 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.

  2. Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye.

  3. Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa.

  4. Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila,

  5. kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”

  6. Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau.

  7. Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana.

  8. Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”

  9. Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.”

  10. Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.

  11. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.

  12. Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.