Tsallake zuwa abun ciki

Ahinoam

6 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ahinoam

  1. Dawuda a lokacin ya riga ya auri Ahinowam daga Yezireyel, dukansu suka zama matansa.

  2. Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel.

  3. An kama matan Dawuda, wato, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal mutumin Karmel wanda ya rasu.

  4. Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel.

  5. An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;

  6. Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;