- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Achish
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat.
Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa, “Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”
Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai.
Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa.
Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina?
Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?”
Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Wata rana Shawulu zai kashe ni, abu mafi kyau da zan yi shi ne in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Da haka Shawulu zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila, a can kuwa zan tsira daga hannunsa.”
Sai Dawuda tare da mutanensa, mutum ɗari shida suka tashi suka haye zuwa wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat.
Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel.
Da Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya gudu zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.
Sai Dawuda ya ce wa Akish, “In na sami tagomashi a gabanka ka ba ni wani wuri a cikin biranenka in zauna a can. Don me bawanka zai kasance tare da kai a gidan sarauta?”
A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda.
Dawuda ya zauna a yankin Filistiyawa shekara ɗaya da wata huɗu.
Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.)
Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish.
Idan Akish ya ce, “Ina ka kai hari yau?” Sai Dawuda yă ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuda, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb na Keniyawa.”
Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa.
Akish ya amince da Dawuda sosai, har ya ce wa kansa, “Ga shi ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama bawana har abada.”
Filistiyawa suka tattara sojojinsu domin su yaƙi Isra’ila. Akish ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
Dawuda ya ce, “Kai da kanka za ka ga abin da bawanka zai yi.” Akish ya ce, “Da kyau, zan sa ka zama mai kāre ni.”
Filistiyawa suka tattara dukan rundunoninsu a Afek. Isra’ila kuwa suka yi sansani kusa da maɓulɓular da take Yezireyel.
Sa’ad da sarakuna Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari-ɗari da na dubu-dubu. Dawuda da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.
Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.”
Amma komandodin Filistiyawa suka yi fushi, suka ce, “Ka sa mutumin nan yă koma zuwa wurin da ka ba shi yă zauna. Ba zai bi mu zuwa wurin yaƙi ba. Yana iya juya a kanmu lokacin yaƙin. Zai iya yin amfani da wannan zarafi yă ciccire kawunanmu don yă faranta wa maigidansa rai?
Tuna fa, ba shi ne Dawuda ɗin da ake girmama da rawa da waƙoƙi ana cewa, “ ‘Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa dubbun dubbai ba’?”