Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountains: Of the church of God

4 ayoyi · 82 fannoni

Ayoyi game da Of the church of God

  1. A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.

  2. Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya.

  3. “A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada.

  4. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.”