Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountains: Gilboa
Ayoyi game da Gilboa
Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Isra’ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka kuma karkashe da yawa a dutsen Gilbowa.
Saurayin ya ce, “Ina kan dutsen Gilbowa a lokacin sai na ga Shawulu jingine a māshinsa. Kekunan yaƙi da mahayansu suna matsowa kusa da shi.
“Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba.