Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Moabites

122 ayoyi · 56 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suka auri mata Mowabawa, sunan ɗaya Orfa ɗayan kuma Rut. Bayan sun zauna a can kamar shekara goma,

  2. Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.

  3. Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?”

  4. Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.

  5. Haka kuma Dawuda ya ci Mowabawa. Ya sa suka kwanta a ƙasa, ya kuma auna su da igiya. Kowane awo biyu ya sa a kashe su, amma awo na uku sai yă sa a bar su da rai. Saboda haka Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka kuma kawo masa haraji.

  6. wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

  7. Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

  8. Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa.

  9. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.

  10. Bayan mutuwar Ahab, Mowab ta yi wa Isra’ila tawaye.

  11. Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari.

  12. Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye.

  13. To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila.

  14. Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”

  15. Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

  16. Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

  17. Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Mene! Ubangiji ya kira mu sarakunan nan uku don kawai yă ba da mu ga Mowab ne?”

  18. Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?” Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.”

  19. Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.

  20. Elisha ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan mahaifinka da annabawa mahaifiyarka.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “A’a, ai Ubangiji ne ya kira mu, mu sarakunan nan uku don yă bashe mu ga Mowab.”

  21. Sai Elisha ya ce, “Muddin Ubangiji Maɗaukaki yana a raye, wanda nake bauta, da ba don ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuda ba, da ko kallonka ba zan yi ba.

  22. Amma yanzu, a kawo mini makaɗin garaya.” Yayinda makaɗin garayan yake kiɗa, ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha

  23. ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, zan cika kwarin nan da tafkunan ruwa.

  24. Gama ga abin da Ubangiji ya ce, ko da yake babu iska, ko ruwan sama, duk da haka kwarin nan zai cika da ruwa, har ku da dabbobinku da kuma sauran dabbobi ku sha.

  25. Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji; zai kuma ba da Mowab a gare ku.