- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Moabites
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
A wannan rana aka karanta Littafin Musa da ƙarfi a kunnuwan mutane aka kuma sami an rubuta cewa kada a karɓi mutumin Ammon ko mutumin Mowab cikin taron Allah,
domin ba su taryi Isra’ila da abinci da ruwa ba amma suka yi hayar Bala’am don yă kira la’ana a kansu. (Amma Allahnmu, ya mai da la’anar ta zama albarka.)
Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.
tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,
Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.
Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne, An lalatar da Ar a Mowab, an hallaka ta da dare! An lalatar da Kir a Mowab, an hallaka ta da dare!
Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu.
A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka.
Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi, aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz. Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi, har zuciyarsu ta karai.
Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu.
Ruwayen Nimrim sun ƙafe ciyayin kuma sun bushe; tsire-tsire duk sun ɓace babu sauran ɗanyen abu.
Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.
Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab; kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim, makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim.
Ruwayen Dimon sun cika da jini, amma zan yi ƙari a kan Dimon, zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.
Ku aiko da raguna a matsayin haraji ga mai mulkin ƙasar, daga Sela a hamada, zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
Kamar tsuntsaye masu firiya da aka kora daga sheƙa, haka matan Mowab suke a kogunan Arnon.
“Ku ba mu shawara, ku yanke shawara. Ku mai da inuwarku kamar dare, a tsakar rana. Ku ɓoye masu gudun hijira, kada ku bashe masu neman mafaka.
Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku; ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.” Mai danniya zai zo ga ƙarshe hallaka kuma za tă daina; masu lalatar da ƙasa za su kare
Da ƙauna za a kafa kursiyi; da aminci mutum zai zauna a kansa, wani daga gidan Dawuda, wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya ya hanzarta yin adalci.
Mun ji fariyar Mowab, mun ji yawan fariyarta da girmankanta, fariyarta da reninta, amma taƙamarsu ta banza ce.
Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi, za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab. Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.
Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.
An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.
Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.