Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Moabites

122 ayoyi · 56 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu, tana gajiyar da kanta ne kawai; sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a, babu wani amfani.

  2. Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab.

  3. Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta, ’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”

  4. Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.

  5. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  6. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.

  7. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’

  8. Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa.

  9. “Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba.

  10. “Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’

  11. Hukunci ya zo wa tudu, zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,

  12. zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,

  13. zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,

  14. zuwa Keriyot da Bozra zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.

  15. “Ku bugar da ita domin ta tayar wa Ubangiji. Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta; bari tă zama abin dariya.

  16. Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba? Ba a kama shi cikin ɓarayi, har kaɗa kai na ba’a kike yi a duka sa’ad da kike magana game da shi?

  17. “Mun ji labarin girman kan Mowab mun ji alfarma girmankanta da kumburinta girmankanta da fariyarta da renin zuciyarta.

  18. Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai ’ya’yanki maza daurin talala ’ya’yanki mata zaman bauta.

  19. “Duk da haka zan maido da wadatar Mowab a kwanaki masu zuwa,” in ji Ubangiji. A nan hukuncin Mowab ya ƙare.

  20. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,”

  21. saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar.

  22. Ya ku mutanena, ku tuna abin da Balak sarkin Mowab ya ƙulla da kuma amsar da Bala’am ɗan Beyor ya bayar. Ku tuna da tafiyarku daga Shittim zuwa Gilgal, don ku san ayyukan adalcin Ubangiji.”