Tsallake zuwa abun ciki

Edom

80 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Idumea, Syria

30.7300, 35.6000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Edom

Tace bisa littafi
  1. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

  2. Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?

  3. Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.

  4. Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”

  5. Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”

  6. Edom, Mowab da Ammon;

  7. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  8. Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu,

  9. Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne?

  10. “Edom za tă zama abin tsoro; dukan wanda ya wuce zai giggice ya yi tsaki saboda dukan mikinta.

  11. Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom, abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman. Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.

  12. Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda.

  13. Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.

  14. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.

  15. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka,

  16. saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi.

  17. Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  18. “Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

  19. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  20. ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’

  21. Zai kuma mamaye Kyakkyawa Ƙasa. Ƙasashe masu yawa za su fāɗi, amma Edom, Mowab da kuma shugabannin Ammon za su kuɓuta daga hannunsa.

  22. Amma Masar za tă zama kango, Edom kuma hamada marar amfani, saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.

  23. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom,

  24. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,

  25. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.