Tsallake zuwa abun ciki

Edom

80 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Idumea, Syria

30.7300, 35.6000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Edom

Tace bisa littafi
  1. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku.

  2. Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom.

  3. A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom.

  4. Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom.

  5. Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki.

  6. Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?” Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

  7. Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

  8. Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.

  9. Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa.

  10. Da sarkin Mowab ya ga yaƙi ya rinjaye shi, sai ya ɗauki mutane masu takobi ɗari bakwai, ya ratsa zuwa wajen sarkin Edom, amma ba su yi nasara ba.

  11. A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki.

  12. Har yă zuwa yau, Edom tana yi wa Yahuda tawaye. A lokaci ɗaya ne Libna ma ta yi tawaye.

  13. Tabbatacce ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana ɗaga kai. To, ka gode da darajar da ka samu, amma ka zauna a gida! Don me kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da kuma ta Yahuda?”

  14. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

  15. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet

  16. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.

  17. Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.

  18. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.

  19. Sa’an nan Solomon ya tafi Eziyon Geber da Elot a bakin tekun Edom.

  20. Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi).

  21. Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.

  22. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

  23. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

  24. Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?

  25. tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,