Skip to content

Zeruiah

25 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Zeruiah

  1. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

  2. Yowab wanda ake ce mamarsa Zeruhiya tare da waɗansu mutanen Dawuda suka fito suka haɗu da su tafkin Gibeyon, Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe.

  3. ’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.

  4. A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”

  5. Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi;

  6. Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom.

  7. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”

  8. Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ”

  9. Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab.

  10. Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”

  11. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”

  12. Dawuda ya ce, “Me ya haɗa ni da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya? Yau ɗin nan kun zama maƙiyana! Ya kamata a kashe wani a Isra’ila a yau? Ban san cewa yau ni sarki ne a bisa Isra’ila ba?”

  13. Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.”

  14. Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.

  15. Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,

  16. Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya.

  17. “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.

  18. Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!”

  19. ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.

  20. Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.

  21. Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,

  22. Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

  23. Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;

  24. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.

  25. Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.