Skip to content

Salt

5 verses

31.0800, 35.3800 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Salt

  1. Dawuda kuwa ya ƙara zama shahararre bayan ya dawo daga kai wa ƙasar Aram hari, daga nan sai ya je ya karkashe mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

  2. Shi ne kuma wanda ya ci mutanen Edom dubu goma a yaƙi, a Kwarin Gishiri, ya kuma ci Sela da yaƙi, ya ba ta suna Yokteyel, sunan da ake kiranta har wa yau.

  3. Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.

  4. Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma.

  5. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!