Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Lamentations

25 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

  2. Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.

  3. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.

  4. “Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila

  5. ka ce, “ ‘Mahaifiyarki zakanya ce cikin zakoki! Takan kwanta cikin ’yan zakoki ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.

  6. Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta, ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.

  7. Al’ummai suka ji labarinsa, aka kuma kama shi cikin raminsu. Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa ƙasar Masar.

  8. “ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba, abin da take fata gani ya tafi, sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta ta mai da shi zaki mai ƙarfi.

  9. Ya yi ta yawo a cikin zakoki, gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi. Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta yakan kuma cinye mutane.

  10. Ya rurrushe kagaransu ya kuma ragargaza biranensu. Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta sun tsorata da jin rurinsa.

  11. Sai al’ummai suka tayar masa, waɗannan daga yankunan da suke kewaye. Suka yafa raga dominsa ya kuwa fāɗa cikin raminsu.

  12. Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji suka kawo shi wurin sarkin Babilon. Suka sa shi cikin kurkuku, saboda haka ba a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila ba.

  13. “ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi da aka shuka kusa da ruwa; ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassa saboda yalwan ruwa.

  14. Rassanta suka yi ƙarfi, suka dace da sandar mai mulki. Ta yi tsayi zuwa sama ana ganin ta saboda tsayinta da kuma saboda yawan rassanta.

  15. Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su.

  16. Yanzu an shuka ta a hamada, a busasshiyar ƙasa marar ruwa.

  17. Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”

  18. “Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau.

  19. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su.

  20. An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.

  21. Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka.

  22. Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta.

  23. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.

  24. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.

  25. Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”