Tsallake zuwa abun ciki

Joab

120 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joab

Tace bisa littafi
  1. Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”

  2. Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni.

  3. Sa’ad da wani daga cikin mutanen ya gan haka, sai ya gaya wa Yowab, “Na ga Absalom yana rataye a itacen oak.”

  4. Yowab ya ce wa mutumin da ya ba shi labarin, “Mene! Ka ga shi? Don me ba ka buge shi har ƙasa nan da nan ba? Ai, da na ba ka shekel goma na azurfa da abin ɗamarar jarumi.”

  5. Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’

  6. Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak.

  7. Masu ɗaukan kayan yaƙin Yowab goma kuwa sun kewaye Absalom, suka bubbuge shi suka kashe.

  8. Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, sai sojoji suka bar fafaran Isra’ila, gama Yowab ya tsai da su.

  9. Yowab ya ce, “Ba kai ba ne za ka kai wannan labari a yau ba. Kana iya kai labarin wani lokaci, amma yau kam ba zai yiwu ba, saboda ɗan sarki ya mutu.”

  10. Sai Yowab ya ce wa wani mutumin Kush, “Je ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Mutumin Kush ɗin kuwa ya rusuna wa Yowab, sai ya ruga a guje.

  11. Ahimawaz ɗan Zadok ya sāke ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru, ina roƙonka bari in bi bayan mutumin Kush nan.” Amma Yowab ya ce, “Ɗana me ya sa kake so ka je? Ba ka da labarin da zai jawo maka lada.”

  12. Sai sarki ya ce, “Saurayin nan Absalom yana nan da rai?” Ahimawaz ya ce, “Na ga wani babban rikicewar a daidai lokacin da Yowab yake gab da aikan bawan sarki da kuma ni, sai dai ban san ko mene ne ba.”

  13. Aka faɗa wa Yowab cewa, “Sarki yana kuka, yana kuma makoki saboda Absalom.”

  14. Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan ’ya’yanka maza, da na ’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka.

  15. Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”

  16. Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.

  17. Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi.

  18. Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba.

  19. Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.

  20. Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!”

  21. Bayan an ɗauke Amasa daga hanya, sai dukan mutane suka bi Yowab don fafaran Sheba ɗan Bikri.

  22. Sai dukan rundunonin da suke tare da Yowab suka zo suka yi wa Sheba kwanton ɓauna a Abel-Bet-Ma’aka. Suka tara ƙasa kewaye da jikin katangar birnin daidai da tsayinta. Sa’an nan waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe katangar.

  23. Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.”

  24. Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.”

  25. Yowab ya ce, “Allah yă sawwaƙe! Allah yă sawwaƙe in hallaka, ko in lalace gādon Ubangiji.