Skip to content

Absalom

92 ayoyi · 23 'yan gida

An kuma san shi da: Abishalom

Ayoyin da suka ambaci Absalom

Tace bisa littafi
  1. na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;

  2. Ana nan sai Amnon ɗan Dawuda ya fara son Tamar, kyakkyawar ’yar’uwar Absalom ɗan Dawuda.

  3. Ya tambayi Amnon ya ce, “Don me kowace safiya fuskarka a ɓace take? Kai ba yaron sarki ba ne? Faɗa mini, me ke faruwa?” Amnon ya ce masa, “Ina son Tamar ƙanuwar wan nawa Absalom ne.”

  4. Absalom ɗan’uwanta ya ce mata, “Amnon, ɗan’uwanki ya ɓata ki ko? To, ki yi shiru ’yar’uwata; ai, ɗan’uwanki ne. Kada wannan abu yă dame ki.” Tamar kuwa ta zauna a gidan ɗan’uwanta Absalom, zaman kaɗaici.

  5. Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.

  6. Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can.

  7. Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”

  8. Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.

  9. Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”

  10. Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran ’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.

  11. Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”

  12. Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.

  13. Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan ’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”

  14. Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar ’yar’uwansa fyaɗe.

  15. Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu. To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.”

  16. Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.

  17. Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku.

  18. Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.

  19. Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom.

  20. Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.”

  21. Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima.

  22. Amma sarki ya ce, “Yă tafi gidansa; kada yă zo yă gan ni.” Saboda haka Absalom ya tafi gidansa, bai kuwa je ganin sarki ba.

  23. A cikin dukan Isra’ila babu wanda ake yabon kyansa kamar Absalom. Tun daga kansa har zuwa tafin ƙafansa babu tabo a jikinsa.

  24. Aka haifa wa Absalom ’ya’ya uku maza da ’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai.

  25. Absalom ya zauna a Urushalima shekara biyu amma ba tare da ganin fuskar sarki ba.