Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Council

44 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ahitofel ya ce wa Absalom, “Zan zaɓi mutum dubu goma sha biyu su fita a daren nan in fafari Dawuda.

  2. Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya. Zan firgita shi, mutanen da suke tare da shi kuwa za su gudu. Sarki ne kaɗai zan kashe

  3. in dawo da dukan mutanen a gare ka. Mutuwar wanda kake nema zai zama dawowar duka; dukan mutanen ba za su cutu ba.”

  4. Wannan shawara ta gamshi Absalom da dukan dattawan Isra’ila.

  5. Amma Absalom ya ce, “A kira mini Hushai mutumin Arkitawan nan shi ma, mu ji abin da zai ce.”

  6. Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.”

  7. Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau.

  8. Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba.

  9. Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’

  10. Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

  11. “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama.

  12. Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai.

  13. In ma ya janye zuwa cikin birni, sai dukan Isra’ila su kawo igiyoyi wa wannan birni, su ja shi zuwa kwari yă wargaje, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

  14. Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa.

  15. Hushai ya ce wa Zadok da Abiyatar, firistoci, “Ahitofel ya ba wa Absalom da dattawan Isra’ila shawara su yi kaza da kaza, amma na ba su shawara su yi haka, su yi haka.

  16. Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”

  17. Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.

  18. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.

  19. Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.

  20. Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”

  21. Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.

  22. Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.

  23. Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.

  24. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.

  25. To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?