Skip to content

Adonijah

24 ayoyi · 22 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Adonijah

  1. na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;

  2. Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa.

  3. Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya.

  4. Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba.

  5. Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,

  6. Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba?

  7. Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’

  8. Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba.

  9. Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka?

  10. Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’

  11. Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?”

  12. Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.”

  13. Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki.

  14. A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse.

  15. Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe.

  16. Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’ ”

  17. To, sai Adoniya, ɗan Haggit ya tafi wurin Batsheba mahaifiyar Solomon. Ita kuwa ta tambaye shi ta ce, “Lafiya?” Ya amsa ya ce, “I, lafiya.”

  18. Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa.

  19. Saboda haka sai ta ce, “Ka sa a ba wa ɗan’uwanka Adoniya, Abishag mutuniyar Shunam tă zama matarsa.”

  20. Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!”

  21. Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba!

  22. Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!”

  23. Sa’ad da labarin ya kai wurin Yowab, wanda ya haɗa kai da Adoniya, ko da yake bai haɗa kai da Absalom ba, sai ya gudu zuwa tentin Ubangiji, ya kama ƙahonin bagade ya riƙe.

  24. na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;