Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sama’ila 2:24kusan 1053 K.H.

    Amma Yowab da Abishai suka fafari Abner, kuma da rana tana fāɗuwa sai suka iso tudun Amma, kusa da Giya, a hanyar zuwa jejin Gibeyon.

  2. 2 Sama’ila 2:25kusan 1053 K.H.

    Sa’an nan mutanen Benyamin suka haɗa kansu suka koyi bayan Abner. Suka zama ƙungiya guda, suka tsaya daram a kan tudu.

  3. 2 Sama’ila 2:26kusan 1053 K.H.

    Sai Abner ya kira Yowab ya ce, har abada ne māshi zai yi ta hallakarwa? Ba ka sani cewa ƙarshen zai zama da ɗaci ba. Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina fafaran ’yan’uwansu?

  4. 2 Sama’ila 2:27kusan 1053 K.H.

    Yowab ya ce, “Muddin Allah yana a raye, da ba a ce ka yi magana ba, da mutanen za su ci gaba da fafaran ’yan’uwansu har gari yă waye.”

  5. 2 Sama’ila 2:28kusan 1053 K.H.

    Sai Yowab ya busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka tsaya; suka daina fafaran Isra’ila. Nan take faɗan ya tsaya.

  6. 2 Sama’ila 2:29kusan 1053 K.H.

    Abner da mutanensa suka ratsa kwarin Urdun dukan dare. Sa’an nan suka haye kogin, suka kuwa ci gaba dukan safe har suka zo Mahanayim.

  7. 2 Sama’ila 2:30kusan 1053 K.H.

    Da Yowab ya dawo daga fafaran Abner, sai ya tattara dukan mutanensa. Ban da Asahel, sai ya gane an rasa mutum goma sha tara na Dawuda.

  8. 2 Sama’ila 2:31kusan 1053 K.H.

    Amma mutanen Dawuda sun kashe mutum ɗari uku da sittin daga kabilar Benyamin da suke tare da Abner.

  9. 2 Sama’ila 2:32kusan 1053 K.H.

    Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.

  10. 2 Sama’ila 3:1kusan 1048 K.H.

    Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.

  11. 2 Sama’ila 3:2kusan 1048 K.H.

    An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;

  12. 2 Sama’ila 3:3kusan 1048 K.H.

    na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;

  13. 2 Sama’ila 3:4kusan 1048 K.H.

    na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;

  14. 2 Sama’ila 3:5kusan 1048 K.H.

    na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.

  15. 2 Sama’ila 3:6kusan 1048 K.H.

    Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.

  16. 2 Sama’ila 3:7kusan 1048 K.H.

    To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”

  17. 2 Sama’ila 3:8kusan 1048 K.H.

    Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?

  18. 2 Sama’ila 3:9kusan 1048 K.H.

    Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.

  19. 2 Sama’ila 3:10kusan 1048 K.H.

    Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”

  20. 2 Sama’ila 3:11kusan 1048 K.H.

    Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.

  21. 2 Sama’ila 3:12kusan 1048 K.H.

    Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”

  22. 2 Sama’ila 3:13kusan 1048 K.H.

    Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”

  23. 2 Sama’ila 3:14kusan 1048 K.H.

    Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”

  24. 2 Sama’ila 3:15kusan 1048 K.H.

    Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.

  25. 2 Sama’ila 3:16kusan 1048 K.H.

    Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.