- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 4:3kusan 1048 K.H.
domin mutanen Beyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.
- 2 Sama’ila 4:4kusan 1048 K.H.
(Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)
- 2 Sama’ila 4:5kusan 1048 K.H.
To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.
- 2 Sama’ila 4:6kusan 1048 K.H.
Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.
- 2 Sama’ila 4:7kusan 1048 K.H.
Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba.
- 2 Sama’ila 4:8kusan 1048 K.H.
Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.”
- 2 Sama’ila 4:9kusan 1048 K.H.
Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,
- 2 Sama’ila 4:10kusan 1048 K.H.
sa’ad da wani mutum ya ce mini, ‘Shawulu ya mutu,’ yana tsammani ya kawo labari mai daɗi ne, na kama shi na kashe a Ziklag. Ladar da na ba shi ke nan saboda labarinsa!
- 2 Sama’ila 4:11kusan 1048 K.H.
Balle fa, sa’ad da mugayen mutane suka kashe marar laifi a gidansa, a bisa gadonsa, ashe, ba zan nemi jininsa daga hannunku in kawar da ku a duniya ba!”
- 2 Sama’ila 4:12kusan 1048 K.H.
Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.
- 2 Sama’ila 5:1kusan 1048 K.H.
Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne.
- 2 Sama’ila 5:2kusan 1048 K.H.
A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ”
- 2 Sama’ila 5:3kusan 1048 K.H.
Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.
- 2 Sama’ila 5:4kusan 1048 K.H.
Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in.
- 2 Sama’ila 5:5kusan 1048 K.H.
A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.
- 2 Sama’ila 5:6kusan 1048 K.H.
Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”
- 2 Sama’ila 5:7kusan 1048 K.H.
Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.
- 2 Sama’ila 5:8kusan 1048 K.H.
A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”
- 2 Sama’ila 5:9kusan 1048 K.H.
Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.
- 2 Sama’ila 5:10kusan 1048 K.H.
Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi.
- 2 Sama’ila 5:11kusan 1048 K.H.
To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.
- 2 Sama’ila 5:12kusan 1048 K.H.
Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya naɗa shi sarki bisa Isra’ila, ya kuma ɗaukaka masarautarsa saboda mutanensa Isra’ila.
- 2 Sama’ila 5:13kusan 1048 K.H.
Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata.
- 2 Sama’ila 5:14kusan 1048 K.H.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
- 2 Sama’ila 5:15kusan 1048 K.H.
Ibhar, Elishuwa, Nefeg, Yafiya,