Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings: Confidence in God

6 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Confidence in God

  1. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

  2. Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

  3. yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa.

  4. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.

  5. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba.

  6. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.