Skip to content

Pharaoh

63 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Pharaoh

Tace bisa littafi
  1. To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.

  2. Fir’auna ya yi fushi da hafsoshin nan nasa guda biyu, shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya,

  3. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.

  4. Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku.

  5. A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.”

  6. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”

  7. Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ya yi mafarki. A mafarkin, ya ga yana tsaye kusa da Nilu,

  8. Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka.

  9. Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.

  10. Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu.

  11. Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau an tuna mini da kāsawata.

  12. Sai ya ci gaba ya ce, Fir’auna ya taɓa husata da bayinsa, ya kuma jefa ni da shugaban masu tuya a cikin kurkuku a gidan shugaban masu tsaro.

  13. Sai Fir’auna ya aika a kawo Yusuf, aka kuwa kawo shi da sauri daga kurkuku. Sa’ad da ya yi aski, ya kuma canja tufafinsa, sai ya zo gaban Fir’auna.

  14. Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Na yi mafarki, kuma babu wanda ya iya fassara shi. Amma na ji an ce sa’ad da ka ji mafarki, kana iya fassara shi.”

  15. Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba ni ne da iyawar ba, Allah zai iya ba wa Fir’auna amsar da yake nema.”

  16. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “A cikin mafarkina, na ga ina tsaye a bakin Nilu,

  17. Sai Yusuf ya ce wa Fir’auna, “Mafarkan Fir’auna, ɗaya ne. Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin yi.

  18. “Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna cewa Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin yi.

  19. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.

  20. “Yanzu fa, bari Fir’auna yă nemi mutum mai basira da kuma hikima, yă sa shi yă shugabanci ƙasar Masar.

  21. Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci.

  22. Ya kamata su tara dukan abincin waɗannan shekaru masu kyau da suke zuwa, su yi ajiyar hatsin a ƙarƙashin ikon Fir’auna, don a ajiye a birane don abinci.

  23. Shirin ya yi wa Fir’auna da kuma dukan hafsoshinsa kyau.

  24. Saboda haka Fir’auna ya tambaye su, “Za mu iya samun wani kamar wannan mutum, wannan wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”

  25. Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya ba ka sanin dukan waɗannan, babu wani mai basira da kuma hikima kamar ka.