Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dreams

92 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”

  2. Abimelek dai bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ya Ubangiji za ka hallaka al’umma marar laifi?

  3. Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.”

  4. Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba.

  5. Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.”

  6. Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.

  7. Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.

  8. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”

  9. Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.

  10. Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”

  11. sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa.

  12. Sa’ad da Yusuf ya zo wurinsu kashegari, sai ya ga duk sun damu.

  13. Saboda haka ya tambayi hafsoshin Fir’auna, waɗanda suke a kurkuku tare da shi, a gidan maigidansa ya ce, “Me ya sa fuskokinku suke a ɓace haka?”

  14. Sai suka amsa, “Mu biyu, mun yi mafarki, amma babu wani da zai fassara mana su.” Sa’an nan Yusuf ya ce musu, “Fassara ba daga Allah take zuwa ba? Ku faɗa mini mafarkanku.”

  15. Sai shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusuf mafarkinsa. Ya ce masa, “A cikin mafarkina, na ga kuringa a gabana,

  16. kuma a kuringar, akwai rassa uku. Nan da nan kuringar ta yi toho, ta huda, ta kuma yi nonna har suka nuna, suka zama inabi.

  17. Kwaf Fir’auna kuwa yana a hannuna, na kuma ɗiba inabin na matse su cikin kwaf Fir’auna, na kuma sa kwaf ɗin a hannunsa.”

  18. Yusuf ya ce masa, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Rassan nan uku, kwana uku ne.

  19. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fitar da kai, yă maido da kai a matsayinka, za ka kuwa sa kwaf Fir’auna cikin hannunsa, kamar yadda ka saba yi sa’ad da kake mai riƙon kwaf nasa.

  20. Amma fa, sa’ad da kome ya zama maka da kyau, ka tuna da ni, ka kuma yi mini alheri, ka ambace ni wa Fir’auna, ka fid da ni daga wannan kurkuku.

  21. Gama da ƙarfi ne aka ɗauke ni daga ƙasar Ibraniyawa, ko a nan ma ban yi wani abin da ya cancanci a sa ni cikin kurkuku ba.’ ”

  22. Sa’ad da shugaban masu tuya ya ga cewa Yusuf ya ba da fassara mai gamsarwa, sai ya ce, wa Yusuf, “Ni ma na yi mafarki. A kaina, akwai kwanduna uku na burodi.

  23. A kwandon na bisa, akwai kayan iri-iri da aka toya, masu kyau domin Fir’auna, amma tsuntsaye suka ci su a kwandon da yake kaina.”

  24. Yusuf ya ce, “Ga abin da mafarkin yake nufi, ‘Kwanduna uku, kwanaki uku ne.

  25. Cikin kwana uku, Fir’auna zai fid da kai, yă rataye ka a kan itace. Tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.’ ”