Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 1:26kusan 1015 K.H.

    Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba.

  2. 1 Sarakuna 1:27kusan 1015 K.H.

    Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?”

  3. 1 Sarakuna 1:28kusan 1015 K.H.

    Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa.

  4. 1 Sarakuna 1:29kusan 1015 K.H.

    Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa,

  5. 1 Sarakuna 1:30kusan 1015 K.H.

    tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.”

  6. 1 Sarakuna 1:31kusan 1015 K.H.

    Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!”

  7. 1 Sarakuna 1:32kusan 1015 K.H.

    Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki,

  8. 1 Sarakuna 1:33kusan 1015 K.H.

    sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon.

  9. 1 Sarakuna 1:34kusan 1015 K.H.

    A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’

  10. 1 Sarakuna 1:35kusan 1015 K.H.

    Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.”

  11. 1 Sarakuna 1:36kusan 1015 K.H.

    Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka.

  12. 1 Sarakuna 1:37kusan 1015 K.H.

    Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!”

  13. 1 Sarakuna 1:38kusan 1015 K.H.

    Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon.

  14. 1 Sarakuna 1:39kusan 1015 K.H.

    Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!”

  15. 1 Sarakuna 1:40kusan 1015 K.H.

    Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.

  16. 1 Sarakuna 1:41kusan 1015 K.H.

    Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?”

  17. 1 Sarakuna 1:42kusan 1015 K.H.

    Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.”

  18. 1 Sarakuna 1:43kusan 1015 K.H.

    Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki.

  19. 1 Sarakuna 1:44kusan 1015 K.H.

    Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki,

  20. 1 Sarakuna 1:45kusan 1015 K.H.

    Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan.

  21. 1 Sarakuna 1:46kusan 1015 K.H.

    Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu.

  22. 1 Sarakuna 1:47kusan 1015 K.H.

    Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa

  23. 1 Sarakuna 1:48kusan 1015 K.H.

    ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ”

  24. 1 Sarakuna 1:49kusan 1015 K.H.

    A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse.

  25. 1 Sarakuna 1:50kusan 1015 K.H.

    Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe.