- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 970–930 BC
Solomon & The Temple
Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Tarihi 1:1kusan 1015 K.H.
Solomon ɗan Dawuda ya kafa kansa sosai a bisa masarautarsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi ya kuma sa ya zama mai girma sosai.
- 2 Tarihi 1:2kusan 1015 K.H.
Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai,
- 2 Tarihi 1:3kusan 1015 K.H.
Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada.
- 2 Tarihi 1:4kusan 1015 K.H.
Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.
- 2 Tarihi 1:5kusan 1015 K.H.
Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can.
- 2 Tarihi 1:6kusan 1015 K.H.
Solomon ya haura zuwa bagaden tagulla a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada, ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa dubbai a kansa.
- 2 Tarihi 1:7kusan 1015 K.H.
A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.”
- 2 Tarihi 1:8kusan 1015 K.H.
Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa.
- 2 Tarihi 1:9kusan 1015 K.H.
To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa.
- 2 Tarihi 1:10kusan 1015 K.H.
Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”
- 2 Tarihi 1:11kusan 1015 K.H.
Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki,
- 2 Tarihi 1:12kusan 1015 K.H.
saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”
- 2 Tarihi 1:13kusan 1015 K.H.
Sa’an nan Solomon ya tafi Urushalima daga masujadar kan tudu a Gibeyon, da kuma daga gaban Tentin Sujada. Ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila.
- 2 Tarihi 1:14kusan 1015 K.H.
Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai, ya kasance da kekunan yaƙi dubu da ɗari huɗu da kuma dawakai dubu goma sha biyu, waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, da kuma tare da shi a Urushalima.
- 2 Tarihi 1:15kusan 1015 K.H.
Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
- 2 Tarihi 1:16kusan 1015 K.H.
Aka shigo da dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye ’yan kasuwan fada suka saye su daga Kuye.
- 2 Tarihi 1:17kusan 1015 K.H.
Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.
- 2 Tarihi 2:1kusan 1015 K.H.
Solomon ya ba da umarni don a gina haikali domin sunan Ubangiji da kuma fada wa kansa.
- 2 Tarihi 2:2kusan 1015 K.H.
Ya ɗebi mutane dubu saba’in su zama ’yan ɗauko, mutane dubu tamanin su zama masu fasa dutse a tuddai, da kuma mutane dubu uku da ɗari shida su zama masu lura da su.
- 2 Tarihi 2:3kusan 1015 K.H.
Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki.
- 2 Tarihi 2:4kusan 1015 K.H.
Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.
- 2 Tarihi 2:5kusan 1015 K.H.
“Haikalin da zan gina zai zama mai girma, domin Allahnmu ya fi dukan sauran alloli girma.
- 2 Tarihi 2:6kusan 1015 K.H.
Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?
- 2 Tarihi 2:7kusan 1015 K.H.
“Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanince a aiki da azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanince da aikin sassaƙa, domin yă yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuda da Urushalima, waɗanda mahaifina Dawuda ya tanada.
- 2 Tarihi 2:8kusan 1015 K.H.
“Ka kuma aika mini al’ul, fir da gumaguman algum daga Lebanon, gama na san cewa mutanenka sun gwanince a yakan katakai a can. Mutanena kuwa za su yi aiki tare da naka