Skip to content

Sheba

17 verses

9.0200, 38.7400 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Sheba

  1. Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,

  2. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.

  3. Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina.

  4. Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba.

  5. Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta.

  6. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.

  7. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina,

  8. Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba.

  9. Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya.

  10. Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.

  11. Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.

  12. Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.

  13. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.

  14. Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.”

  15. “ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.

  16. “ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke.

  17. Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’