Tsallake zuwa abun ciki

Queen of Sheba

8 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Queen of Sheba

  1. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji game da sunan da Solomon ya yi, da kuma dangantakarsa da Ubangiji, sai ta zo tă gwada shi da tambayoyi masu wuya.

  2. Da sarauniya Sheba ta ga dukan hikimar Solomon da fadan da ya gina.

  3. Ta kuma ba sarki talenti 120 na zinariya, da kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa haka kamar yadda sarauniyar Sheba ta ba wa Sarki Solomon ba.

  4. Sarki Solomon ya ba wa sarauniyar Sheba dukan abin da take so, da kuma duk abin da ta nema, ban da abin da ya ba ta daga yalwar fadan sarki. Sa’an nan ta koma tare da tawagarta zuwa ƙasarta.

  5. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.

  6. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina,

  7. Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba.

  8. Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya.