Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 2:23kusan 1014 K.H.

    Sai Sarki Solomon ya rantse da sunan Ubangiji ya ce, “Bari Allah yă yi mini hukunci mai tsanani, idan ban sa Adoniya ya biya wannan roƙo da ransa ba!

  2. 1 Sarakuna 2:24kusan 1014 K.H.

    Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!”

  3. 1 Sarakuna 2:25kusan 1014 K.H.

    Saboda haka Sarki Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada yă kashe Adoniya; ya kuwa kashe shi.

  4. 1 Sarakuna 2:26kusan 1014 K.H.

    Ga Abiyatar firist kuwa sarki ya ce, “Tafi gonarka a Anatot. Ka cancanci ka mutu, amma ba zan kashe ka yanzu ba, domin ka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji Mai Iko Duka a gaban mahaifina Dawuda, ka kuma sha wahala tare mahaifina.”

  5. 1 Sarakuna 2:27kusan 1014 K.H.

    Saboda haka Solomon ya cire Abiyatar daga aikin firist na Ubangiji, ya cika maganar da Ubangiji ya yi a Shilo game da gidan Eli.

  6. 1 Sarakuna 2:28kusan 1014 K.H.

    Sa’ad da labarin ya kai wurin Yowab, wanda ya haɗa kai da Adoniya, ko da yake bai haɗa kai da Absalom ba, sai ya gudu zuwa tentin Ubangiji, ya kama ƙahonin bagade ya riƙe.

  7. 1 Sarakuna 2:29kusan 1014 K.H.

    Aka faɗa wa Sarki Solomon cewa Yowab ya gudu zuwa tentin Ubangiji, yana kuma kusa da bagade. Sai Solomon ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada ya ce, “Je ka kashe shi!”

  8. 1 Sarakuna 2:30kusan 1014 K.H.

    Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’ ” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.”

  9. 1 Sarakuna 2:31kusan 1014 K.H.

    Sai sarki ya umarci Benahiya ya ce, “Yi kamar yadda ya faɗa. Ka kashe shi, ka kuma binne shi, ka wanke ni da gidan mahaifina daga laifin jini marasa laifin da Yowab ya zubar.

  10. 1 Sarakuna 2:32kusan 1014 K.H.

    Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi.

  11. 1 Sarakuna 2:33kusan 1014 K.H.

    Bari alhakin jininsu yă koma a kan Yowab da kuma zuriyarsa har abada. Amma bari salamar Ubangiji tă kasance a kan Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da kuma mulkinsa, har abada.”

  12. 1 Sarakuna 2:34kusan 1014 K.H.

    Sai Benahiya ɗan Yehohiyada ya haura ya bugi Yowab, ya kashe shi, ya kuwa binne shi a gidansa a ƙauye.

  13. 1 Sarakuna 2:35kusan 1014 K.H.

    Sai sarki ya sa Benahiya ɗan Yehohiyada ya zama shugaba a bisa mayaƙa a matsayin Yowab, ya kuma sa Zadok firist a wurin Abiyatar.

  14. 1 Sarakuna 2:36kusan 1014 K.H.

    Sa’an nan sarki ya aika aka kawo Shimeyi, ya kuma ce masa, “Ka gina wa kanka gida a nan a Urushalima, ka zauna a ciki, kada ka kuskura ka tafi wani wuri.

  15. 1 Sarakuna 2:37kusan 1014 K.H.

    Gama ran da ka fita, ka haye Kwarin Kidron, ka tabbata za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”

  16. 1 Sarakuna 2:38kusan 1014 K.H.

    Shimeyi ya amsa wa sarki ya ce, “Abin da ka faɗa yana da kyau. Bawanka zai yi kamar yadda ranka yă daɗe sarki, ya faɗa.” Shimeyi kuwa ya yi zama a Urushalima na dogon lokaci.

  17. 1 Sarakuna 2:39kusan 1011 K.H.

    Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.”

  18. 1 Sarakuna 2:40kusan 1011 K.H.

    Da jin haka, sai ya tashi ya shimfiɗa wa jakinsa abin zama, ya hau, ya tafi Gat wurin Akish domin neman bayinsa. Shimeyi kuwa ya dawo da su gida daga Gat.

  19. 1 Sarakuna 2:41kusan 1011 K.H.

    Da aka faɗa wa Solomon cewa Shimeyi ya bar Urushalima zuwa Gat, har ya dawo.

  20. 1 Sarakuna 2:42kusan 1011 K.H.

    Sai sarki ya aika a kawo Shimeyi, ya ce masa, “Ban sa ka rantse da sunan Ubangiji, na kuma ja maka kunne cewa, ‘A ranar da ka kuskura ka bar nan ka tafi wani wuri, ka tabbata za ka mutu ba’? A lokacin ka ce mini, ‘Abin da ka faɗa yana da kyau. Zan kuwa kiyaye.’

  21. 1 Sarakuna 2:43kusan 1011 K.H.

    To, me ya sa ba ka kiyaye rantsuwar da ka yi ga Ubangiji, ka kuma yi biyayya da umarnin da na ba ka ba?”

  22. 1 Sarakuna 2:44kusan 1011 K.H.

    Sarki ya ce wa Shimeyi, “Ka sani a zuciyarka dukan muguntar da ka yi wa mahaifina Dawuda. Yanzu Ubangiji zai sāka maka saboda muguntarka.

  23. 1 Sarakuna 2:45kusan 1011 K.H.

    Amma za a yi wa Sarki Solomon albarka, sarautar Dawuda kuma za tă kasance a tsare a gaban Ubangiji har abada.”

  24. 1 Sarakuna 2:46kusan 1011 K.H.

    Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi. Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon.

  25. 1 Sarakuna 3:1kusan 1014 K.H.

    Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.