Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 3:27kusan 1014 K.H.

    Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.”

  2. 1 Sarakuna 3:28kusan 1014 K.H.

    Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

  3. 1 Sarakuna 4:1kusan 1014 K.H.

    Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.

  4. 1 Sarakuna 4:2kusan 1014 K.H.

    Waɗannan su ne manyan shugabanninsa. Azariya ɗan Zadok shi ne firist;

  5. 1 Sarakuna 4:3kusan 1014 K.H.

    Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.

  6. 1 Sarakuna 4:4kusan 1014 K.H.

    Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci.

  7. 1 Sarakuna 4:5kusan 1014 K.H.

    Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara.

  8. 1 Sarakuna 4:6kusan 1014 K.H.

    Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.

  9. 1 Sarakuna 4:7kusan 1014 K.H.

    Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.

  10. 1 Sarakuna 4:8kusan 1014 K.H.

    Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;

  11. 1 Sarakuna 4:9kusan 1014 K.H.

    Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;

  12. 1 Sarakuna 4:10kusan 1014 K.H.

    Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);

  13. 1 Sarakuna 4:11kusan 1014 K.H.

    Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);

  14. 1 Sarakuna 4:12kusan 1014 K.H.

    Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;

  15. 1 Sarakuna 4:13kusan 1014 K.H.

    Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);

  16. 1 Sarakuna 4:14kusan 1014 K.H.

    Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;

  17. 1 Sarakuna 4:15kusan 1014 K.H.

    Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);

  18. 1 Sarakuna 4:16kusan 1014 K.H.

    Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;

  19. 1 Sarakuna 4:17kusan 1014 K.H.

    Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;

  20. 1 Sarakuna 4:18kusan 1014 K.H.

    Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;

  21. 1 Sarakuna 4:19kusan 1014 K.H.

    Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.

  22. 1 Sarakuna 4:20kusan 1014 K.H.

    Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki.

  23. 1 Sarakuna 4:21kusan 1014 K.H.

    Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.

  24. 1 Sarakuna 4:22kusan 1014 K.H.

    Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci,

  25. 1 Sarakuna 4:23kusan 1014 K.H.

    shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.