Tsallake zuwa abun ciki

Jeroboam

81 ayoyi · 4 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Jeroboam

Tace bisa littafi
  1. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,

  2. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.

  3. To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai ’yan kwanto su kasance a bayansu.

  4. mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda.

  5. Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.

  6. Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.