Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings: God chooses

3 ayoyi · 175 fannoni

Ayoyi game da God chooses

  1. “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.

  2. Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.

  3. Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa.