Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings

580 ayoyi · 175 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Balle fa, sa’ad da mugayen mutane suka kashe marar laifi a gidansa, a bisa gadonsa, ashe, ba zan nemi jininsa daga hannunku in kawar da ku a duniya ba!”

  2. Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.

  3. Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.

  4. Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada.

  5. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

  6. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

  7. Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”

  8. Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”

  9. Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.”

  10. Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa

  11. Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)

  12. Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki.

  13. Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne.

  14. Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu.

  15. Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu.

  16. Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka.

  17. Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa.

  18. To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’

  19. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka.

  20. Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ”

  21. Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa.

  22. (A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.)

  23. Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya.

  24. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.

  25. Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;