Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Being a man of war not permitted to build

7 ayoyi · 72 fannoni

Ayoyi game da Being a man of war not permitted to build

  1. “Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna?

  2. Ban taɓa zama a gida ba tun daga ranar da na fito da Isra’ilawa daga Masar har yă zuwa yau. Ina dai kai da kawowa a tenti, a matsayin mazaunina.

  3. A cikin kaiwa da kawowar da nake yi cikin dukan Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani shugabanninsu wanda na umarta su lura da mutanena Isra’ila, “Don me ba ku gina mini mazauni da katakon al’ul ba?” ’

  4. “Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila.

  5. Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.

  6. “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  7. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo mini, ‘Ka zub da jini mai yawa ka kuma yi yaƙe-yaƙe masu yawa. Ba za ka gina gida domin Sunana ba, domin ka zub da jini da yawa a duniya a idona.