Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Repaired by Jehoash at the institution of Jehoiada

21 ayoyi · 72 fannoni

Ayoyi game da Repaired by Jehoash at the institution of Jehoiada

  1. Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali.

  2. Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.”

  3. Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba.

  4. Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.”

  5. Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba.

  6. Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin.

  7. Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.

  8. Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,

  9. masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.

  10. Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin Ubangiji ba;

  11. an ba ma’aikatan da suka gyara haikalin ne.

  12. Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji.

  13. Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.

  14. Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”

  15. Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al.

  16. Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji.

  17. Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada.

  18. Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika.

  19. Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.

  20. Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin.

  21. Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi.