Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Filled with the cloud of glory

4 ayoyi · 72 fannoni

Ayoyi game da Filled with the cloud of glory

  1. Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji.

  2. Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa.

  3. Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,

  4. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.