Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Two cherubims of gilded olive wood made within

9 ayoyi · 72 fannoni

Ayoyi game da Two cherubims of gilded olive wood made within

  1. A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma.

  2. Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike.

  3. Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa.

  4. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.

  5. Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin.

  6. Ya dalaye kerubobin da zinariya.

  7. Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.

  8. Haka ma fiffiken kerub na biyu ɗin tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo bangon haikalin, ɗaya fiffiken shi ma tsawonsa kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub na farko.

  9. Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban zauren.