Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Anxious to build

7 ayoyi · 72 fannoni

Ayoyi game da Anxious to build

  1. sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.”

  2. Dawuda ya ce wa Solomon, “Ɗana, na yi niyya a zuciyata in gina gida saboda Sunan Ubangiji Allahna.

  3. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,

  4. Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,

  5. “Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,

  6. ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,

  7. sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”