Skip to content

Michal

16 ayoyi · 11 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Michal

  1. ’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban ’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal.

  2. Mikal ’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce,

  3. Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.

  4. Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,

  5. Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.”

  6. Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere.

  7. Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi.

  8. Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?” Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”

  9. Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim.

  10. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”

  11. Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”

  12. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.

  13. Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”

  14. Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.

  15. Mikal ’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.

  16. Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.