Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Michal

26 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ”

  2. Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.”

  3. Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa.

  4. Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.

  5. Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika,

  6. Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.

  7. Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,

  8. Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo,

  9. Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.

  10. Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.”

  11. Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere.

  12. Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi.

  13. Da Shawulu ya aiki mutane su kama Dawuda. Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.”

  14. Sai Shawulu ya sāke aiki mutanen su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi a gādonsa domin in kashe shi.”

  15. Amma da mutanen suka shiga sai suka ga gunkin a gadon, a wajen kan kuwa akwai gashin akuya.

  16. Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?” Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”

  17. Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim.

  18. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”

  19. Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”

  20. Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.

  21. Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.

  22. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.

  23. Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”

  24. Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.

  25. Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi ’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.”