Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Michal: Rescues David from death

9 ayoyi · 5 fannoni

Ayoyi game da Rescues David from death

  1. Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo,

  2. Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.

  3. Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.”

  4. Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere.

  5. Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi.

  6. Da Shawulu ya aiki mutane su kama Dawuda. Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.”

  7. Sai Shawulu ya sāke aiki mutanen su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi a gādonsa domin in kashe shi.”

  8. Amma da mutanen suka shiga sai suka ga gunkin a gadon, a wajen kan kuwa akwai gashin akuya.

  9. Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?” Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”