Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu.

  2. Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”

  3. Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Wane ni, wa ya san iyayena ko kabilar iyayena a Isra’ila da zan zama surukin sarki?”

  4. Da lokaci ya kai da Merab ’yar Shawulu za tă yi aure da Dawuda, sai aka aurar da ita wa Adriyel na Mehola.

  5. Mikal ’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce,

  6. “Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”

  7. Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’ ”

  8. Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.”

  9. Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa.

  10. Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.

  11. Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika,

  12. Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.

  13. Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda, ’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,

  14. sai Shawulu ya ƙara jin tsoron Dawuda har ya zama maƙiyinsa a dukan sauran rayuwarsa.

  15. Manyan sojojin Filistiyawa suka yi ta fita suna yaƙi da Isra’ilawa, amma kullum Dawuda yakan sami nasara fiye da sauran manyan sojojin Shawulu. Ta haka ya yi suna ƙwarai.

  16. Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai.

  17. Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya.

  18. Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske.

  19. Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”

  20. Ta haka Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan maganarsu. Ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya zauna tare da Shawulu kamar dā.

  21. Wani yaƙi ya sāke tashi, Dawuda kuwa ya fita ya yaƙi Filistiyawa, ya kai musu hari mai tsanani, sai da suka gudu a gabansa.

  22. Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo,

  23. Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.

  24. Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.”

  25. Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere.