Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Ana ciki haka, sai Bafilistin nan shi ma ya fita yana gusowa zuwa wurin Dawuda. Mai riƙe masa garkuwar yaƙi kuwa yana tafe a gabansa.

  2. Bafilistin ya dubi Dawuda daga sama har ƙasa, ya gan dai ɗan yaro ne kawai, kyakkyawa kuma mai ƙoshin lafiya, sai ya rena shi.

  3. Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.

  4. Ya ce, “Zo nan, ni kuwa zan ba da naman jikinka ga tsuntsayen sama da namun jeji su ci.”

  5. Dawuda ya ce wa Bafilistin, “Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.

  6. Yayinda Bafilistin yana matsowa kusa domin yă fāɗa wa Dawuda, sai Dawuda ya ruga a guje zuwa bakin dāgā don yă same shi.

  7. Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.

  8. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara a kan Bafilistin. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

  9. Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.

  10. Dawuda ya ɗauki kan Bafilistin zuwa Urushalima. Sai Dawuda ya ajiye kayan yaƙin Bafilistin a tentinsa.

  11. Yayinda Shawulu yake kallon Dawuda sa’ad da za shi yă yaƙi Bafilistin, sai ya tambayi Abner, komandan rundunarsa ya ce, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya ce ran sarki yă daɗe, “Ban sani ba.”

  12. Dawuda yana dawowa daga karkashe Filistiyawa ke nan, sai Abner ya kai shi gaban Shawulu, riƙe da kan Bafilistin.

  13. Sai Shawulu ya ce, “Kai ɗan wane ne, saurayi?” Dawuda ya ce, “Ni ɗan bawanka Yesse ne, na Betlehem.”

  14. Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.

  15. Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.

  16. Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.

  17. Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.

  18. Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.

  19. Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

  20. Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”

  21. Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.

  22. Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.

  23. Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.

  24. Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.

  25. A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi.