Tsallake zuwa abun ciki

Shammah

5 ayoyi · 9 'yan gida

An kuma san shi da: Shimma, Shimeah, Shimei

Ayoyin da suka ambaci Shammah

  1. Sai Yesse ya sa Shamma yă zo gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ma ba.”

  2. Manyan ’ya’yansa maza uku, sun bi Shawulu wajen yaƙi. Ɗansa na fari shi ne Eliyab, na biyu shi ne Abinadab, na uku kuwa shi ne Shamma.

  3. To, Amnon yana da wani aboki mai suna Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab dai mai wayo ne ƙwarai.

  4. Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar ’yar’uwansa fyaɗe.

  5. Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,