- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Born
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sai Allah ya ce, “Duk da haka dai, matarka Saratu za tă haifi maka ɗa; za ka kuma kira shi Ishaku. A kansa zan tabbatar da madawwamin alkawarina, da kuma ga zuriyarsa da za su zo bayansa.
Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!
Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.”
Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,
Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”
Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.
Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”
Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”
Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ƙidaya dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa maza daga wata ɗaya da kuma fiye ka kuma rubuta sunayensu.
Ka ɗauko mini Lawiyawa a maimakon dukan ’ya’yan fari na Isra’ilawa, haka ma na dabbobi na Lawiyawa, a maimakon ’ya’yan fari na dabbobin Isra’ilawa. Ni ne Ubangiji.”
Haka Musa ya ƙidaya ’ya’yan fari na Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Jimillar ’ya’yan fari maza daga wata ɗaya da kuma fiye, da aka rubuta bisa ga sunayensu, 22,273 ne.
Ka ba wa Haruna da ’ya’yansa kuɗin fansar da ya haura kai na ’ya’yan farin Isra’ilawa.”
Haka, Musa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.
Daga ’ya’yan fari na Isra’ilawa, ya karɓi azurfa masu nauyin shekel 1,365, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
Sa’an nan Musa ya ba da kuɗin fansar ga Haruna da ’ya’yansa, yadda maganar Ubangiji ta umarce shi.
Da isarsu, Sama’ila ya ga Eliyab sai ya yi tsammani shi ne, sai ya ce, “Lalle ga shafaffe na Ubangiji tsaye a gaban Ubangiji.”
Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
Sai Yesse ya kira Abinadab yă zo gaban Sama’ila. Amma Sama’ila ya ce, “Ko wannan ma Ubangiji bai zaɓe shi ba.”
Sai Yesse ya sa Shamma yă zo gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ma ba.”
Yesse ya sa ’ya’yansa maza bakwai suka wuce gaban Sama’ila, amma Sama’ila ya ce masa, “Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.”
Don haka ya tambayi Yesse ya ce, “Su ke nan ’ya’yan maza da kake da su?” Yesse ya ce, “Har yanzu akwai ɗan autan, amma yana kiwon tumaki.” Sama’ila ya ce, “Ka aika yă zo, ba za mu zauna ba sai ya iso.”
Sai ya aika aka kawo shi. Ga shi kuwa kyakkyawan saurayi ne mai kyan gani. Ubangiji ya ce, “Tashi ka shafe shi, shi ne wannan.”
Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.